Jump to content

Wq/ha/Aisha Rateb

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Aisha Rateb
Aisha Rateb

Aisha Rateb (Fabrairu 1928 – 4 Mayu 2013) ta kasance lauya ce, ‘yar siyasa kuma jakadiya mace ta farko a Masar (Egypt). Ta kasance kuma farfesa a fannin dokokin kasa da kasa a Jami’ar Cairo.

Zantuka

[edit | edit source]
  • Domin in samu hakkokina. Na shiga ƙungiyar Huda Shaarawy da wasu ƙungiyoyi da ke fafutukar kare haƙƙin mata. A lokacin ina da shekara 21 kacal, amma ba tare da wani sakamako ba.
  • Ni ce mace ta biyu 'yar Larabawa da ta zama jakada bayan ‘yar sarkin Hassan. Haka kuma, ban kasance jakadiyar farko daga Masar zuwa Turai ba; waɗanda suka rigani su ne Hatshepsut, Nefertari, da Nefertiti, sarakuna mata na Masar da ake jin sunansu a duk duniya.
  • Ba wasu ba ne sakatarori ne waɗanda ke bin umarni kuma ana ba su ayyuka maimakon su kasance ministoci masu ikon ƙirƙirar manufofi.
  • Hana shiga bangaren shari’a bisa la’akari da jinsi ya sabawa Sashe na arba’in na kundin tsarin mulkin Masar, wanda ya bayyana cewa “’yan ƙasa suna da ‘yanci daidai da kuma nauyi daidai, kuma babu wariya a kansu saboda jinsi, asali, harshe ko akida.”