Wq/ha/Aisha Falode
Appearance

Aisha Falode Ƙwararriyar ’yar jarida ce ta wasanni a Najeriya. Hakanan ita ce Shugabar Ƙungiyar Gasar Ƙwallon Ƙafa (Football) ta Mata na kasar Najeriya (NWFL).
Zantuka
[edit | edit source]- Najeriya ta kasance jagora a Afirka wajen ƙwallon ƙafa ta mata. Ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin sauran ƙasashe su fahimci cewa akwai yiwuwar ci gaba ga mata a wannan wasa.
- Kowa yana da halayensa na kansa, amma haɗuwar waɗannan halaye daban-daban ne ke sauƙaƙa aiki tare da kuma sa shi ya zama mai sauƙi da inganci.
- Dole ne ka tabbatar da kanka kuma ka kware sosai a abin da kake yi.
- Yana da muhimmanci mu iya amfana da kuma ƙarfafa juna, kuma yana da daɗi sosai mu san cewa za mu iya dogaro da goyon bayan ƙungiyar mata da ke fuskantar ko kuma suke da irin kalubalen da muke fuskanta.
- Ƙwallon ƙafa, musamman, tana daidaita mutane, kuma mata suna samun wurin su a cikin dimbin damar da wasanni ke bayarwa.
- Mata dole ne su fara son kansu kuma su tanadar da matakalar da sauran mata za su hau.
- Dama ita ce kalmar tsaro. Dole ne mu nufi damar, mu kasance a shirye domin kamasu idan sun bayyana.
- Babu nasara ba tare da sadaukarwa ba. Ba mata kaɗai ba ma, maza ma suna yin manyan sadaukarwa.
- A gaskiya, lokaci yana da wuya, amma lokutan wuyan sukan fitar da mafi alheri daga cikin mutane, ta fuskar ƙirƙira da fasaha.
- Idan ka buga wasa da kyau, ana saka maka da kyauta mai tsoka. Kwallon kafa a Asiya ta fi jan hankali yanzu, duka ta fuskar gasa da kuma riba ta kudi.