Wq/ha/Aisha Buhari
Appearance
Aisha Buhari, ita ce matar tsohon shugaban ƙasar Najeriya,Muhammadu Buhari.
Zantuka
[edit | edit source]- A cire tsoro ayi abinda ya dace.
- Aisha Buhari ta faɗi haka ne a lokacin da take yin martani game da harkokin tsaro da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa a Arewacin Najeriya.
- Ina da ƙwarin gwiwar cewa sha'awarmu ta gaba ɗaya na inganta ilimin ƙananan yara da ƴan mata za ta iya faɗaɗa fiye da yadda take a yanzu.
- Aisha Buhari ta fadi haka a lokacin da take karɓar membobin ƙungiyar masu dillancin magunguna ta ƙasar Amurka (NAPPSA).
- Yara suna da daraja kuma su ne makomarmu. Wajibi ne da alhakinmu a matsayinmu na iyali da al'umma mu nuna ƙauna, kulawa da kuma kare su.
- "Ina da kwarin gwiwar cewa sha'awarmu ta inganta ilimin yara mata za ta iya fadada fiye da yadda take a yanzu."
- [1]Aisha Buhari ta fadi haka ne a lokacin da ta karbi bakuncin mambobin kungiyar likitocin harhada magunguna ta Najeriya (NAPPSA) daga kasar Amurka, wadanda suka kai mata ziyara Abuja.