Wq/ha/Aisha Albasri
Appearance
Aisha Albasri, Fitacciyar marubuciya ce daga Maroko(Marocco), mai rubuta waƙoƙi, littattafai da labarai. Ta samu lambobin yabo da dama a Aljeriya, Faransa, da Hadaddiyar Daular Larabawa(UAE). Aikinta an fassara shi zuwa yarukan Sifaniyanci(Spanish), Faransanci, Italiyanci, Turkiyanci da kuma Turanci.
Zantuka
[edit | edit source]- A kullum akwai buri, kuma kowace rami tana da ƙarshenta. Written by Emad Aldeen in 2021
- Abun ban mamaki shi ne, a lokacin da muke dab da mutuwa, tunani tana ƙara ƙarfi sosai. Muna sake rayuwa tamkar fim da ke farawa daga ƙarshensa. Written by Emad Aldeen in 2021
- Ban san wanda ya ce ba, muna shafe rayuwarmu muna neman wuri mafi dacewa da mutuwa. Youm7 Newspaper
- Ɗaya daga cikin jaruman littafina Layali Alobour na da ra'ayin cewa mutuwa hanya ce kawai zuwa wani irin zama na uku, wanda ba za'a iya kira rayuwa ba ko mutuwa, domin abu ne da ba'a sani ba. Babu wani abu da ke da ƙarshe, ba rayuwa ba, ba mutuwa ba, har ma da abin da ke zuwa bayan mutuwa. Addinai sun yi ƙoƙari ƙwarai da gaske wajen bayar da bayani da sunaye game da wannan zama ta uku, domin kawai su kwantar da hankalin zuciyar ɗan adam. Gardenia Magazine in 2020
- Babu wanda ke jayayya da abin da wannan ƴar Marokon marubuciya kuma ƙwararriyar mace ta cimma a cikin ‘yan shekarun nan, kuma hakan ya bayyanane ta yawan littattafan da ta wallafa, lambobin yabo da ta samu, halartarta a tarukan al’adu, da kuma gudummawar da take bayarwa wajen farfaɗo da harkar al’adu a Maroko da duniyar Larabawa. An Interview With Alittihad
- Yawaitar nau’o’in adabi ƙarin daraja ne ga marubuci. Idan mawaki ya rubuta labari (novel), hakan na ƙara masa wadatar fasaha. Ma’anar rubutu a yau ta faɗaɗa sosai, domin an danganta ta da ‘yancin ƙirƙira da haƙƙin yin tunani da amfani da ƙwazo. An Interview With Alittihad