Wq/ha/Aisha Al Kaabi
Appearance
Aisha Al Kaabi, An haife ta a ranar 8 ga watan Mayu, 1973, a Ajman, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (United Arab Emirates). Ɗaya ce daga cikin ƙwararrun mawaƙan ƙasar Emirati, marubuciyar gajerun labarai, mai fasaha, kuma mai fassara. Ta samu digiri na farko a fannin Kimiyya daga Jami’ar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Zantuka
[edit | edit source]- "Ina son rubuta labarai, kuma ina son ba da labarai. ". Aisha Al-Kaabi ta bayyana jin daɗinta na gaske wajen bayar da labarai, wanda ya samo asali daga tarihin iyalinta a fannin adabi da waka.
- "Buga littattafai nauyi ne ga sabuwar ƙarni, ga ƙasa. ". Sadaukarwarta wajen haɓaka al’adun adabi a Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa, ta mai da hankali kan muhimman ayyuka ga ƙarni mai tasowa, ana nuna shi a cikin wannan jimla.