Wq/ha/Aisha Abubakar Abdulwahab
Appearance
Aisha Abubakar Abdulwahab (An haife ta kimanin shekarar 1971) tsohuwar 'yar sanda ce a Najeriya wadda ta lashe kyautar UNESCO ta mata a fannin kimiyya domin yin karatu kan cutar tarin fuka (tuberculosis). Ta kasance tana kula da shirin tallafin rage raɗaɗi a hedikwatar rundunar ‘yan sanda da ke Abuja a lokacin annobar Corona-virus.
Zantuka
[edit | edit source]- Ni 'yar sanda ce. Ni ce AIG Aishatu Abubakar Baju, amma kuma likita ce ni. Na shiga rundunar 'yan sanda a matsayin likita. Ina matuƙar alfahari da kasancewata 'yar sanda. Haka kuma ni ce Shugabar Hukumar Likitocin Dabbobi ta Najeriya (Veterinary Council of Nigeria). Don haka, ku kira ni da dukkanin muƙaman, Ina son su.
- To, ya danganta da abin da kake son yi a rayuwa. Duk abin da ka ɗauka da muhimmanci, zaka samu hanya ko mafita a kansa.