Wq/ha/Ahmadu Bello Sardauna
Ahmadu Bello, Sardaunan, Sokoto, babban ɗan siyasar Najeriya ne, shugaba, kuma basarake.( An haife shi a ranar sha biyu (12) ga watan Yuni,na shekara ta alif ɗari tara da goma (1910), kuma yana ɗaya daga cikin zuriyar wanda ya kafa Daular Sakkwato. Ya yi aiki a matsayin Firimiya na Arewacin Najeriya daga shekara ta alif dari tara da hamsin da huɗu 1954 har zuwa lokacin da aka kashe shi a shekarar alif ɗari tara da sittin da shida 1966.
A matsayinsa na shugaban jam'iyyar Northern People's Congress (NPC), ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban siyasar Najeriya kafin samun ƴancin kai da kuma a lokacin bayan samun ƴanci. Ahmadu Bello ya shahara wajen ƙoƙarin zamani ci na yankin Arewa ta hanyar inganta ilimi, samar da abubuwan more rayuwa, da kuma bunƙasa noma da kuma bunƙasa tattalin arzikin Arewa.Haka kuma, yana ƙoƙari wajen kare al’adu da ɗabi’un yankin Arewa.
Anan gaba, ana tuna da gaggarumin tasirinsa musamman game da haɗin kan Arewa da ci gaban sa. An kashe shi a juyin mulkin da akayi a shekarar alif ɗari tara da sittin da shida 1966, wanda ya canza yanayin siyasar Najeriya. Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ilimi a Najeriya, an sanya sunanta domin girmamawa a gareshi.
Zantuka
[edit | edit source]- dole ne mu haɗa kanmu wajen ganin mun ciyar da ƙasar mu gaba.