Wq/ha/Adjany Costa
Appearance

Adjany da Silva Freitas Costa (An haife ta 1989) masaniyar biology ce ‘yar Angola, kuma masaniyar Conservation biology daga Huambo wacce tayi aiki a matsayin Ministan Al’adu, Yawon Bude Ido, da kuma Muhalli daga watannin Afurelu zuwa Oktoban 2020.
Zantuka
[edit | edit source]- Dole ne mu sani cewa duk wani sarari na conservative jerin abubuwa ne; ba wai kawai game da wanzuwar rayuwa bane (biodiversity) kawai, ba wai kawai game da mutanen gida bane.
- Duniya ce ruwan-toka wacce inda dole ka kula da duk wani abu da akayi nasara a fannin saboda wannan shine zai baka karfin gwiwa cigaba.
- Abunda ke kara mun karfin gwiwa a yanzu shine al’ummominmu na gida da nayi aiki da su. Duba da kananan matakan da suka dauka ba tare da wani tsararriyar dubara ba ya karamun karfin gwiwar in kara taimakon su.
- Biology ba wani sanannen aiki bane a Angola. Ma’aikatun man fetur da gas sun mamaye kusan kaso 90 na tattalin arzikin kasar, saboda haka, ana kallon wulakanci ga biology, conservation, da kuma sauran ayyukan ilimin halittu. Suna ganin biology da wasu sifofi na Zootopia - ba aiki bane na ainihi. Mutane da dama zasu yi shi ne kawai idan babu wata daman.
- Yana da muhimmanci sosai kuma har ila yau yana da gamsarwa sosai.
- Mafi muhimmancin bangaren aiki na shine daman sanya abunda ya shafi muhalli a batutuwan da mutane ke ji basu da alaka ko kadan.
- A yayinda mutum yake girma matsaloli akan tafarkin aikinshi zasu watsa mafarkin da yake yi, amma su taimaka maka ka gina wani mafarkin na daban. Ina kiran shi ‘mafarki bakigai’.
- Karfafa gwiwa yana yi amma idan baka da juriya, idan baka da mayar da hankali kuma baka da buri, yana da wahala sosai ka cigaba.