Jump to content

Wq/ha/Adeola Fayehun

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Adeola Fayehun

Adeola Eunice Oladele Fayehun, (an haife ta a ranar 6 ga watan Yuli, a shekara ta 1984), ƴar jarida ce ta Najeriya, da ta kware wajen tattaunawa kan batutuwan da suka shafi yanayin siyasa, zamantakewa, da tattalin arziƙi da ke shafar rayuwar yau da kullun na ƴan Afirka mazauna nahiyar.

Zantuka

[edit | edit source]
  • Ko yaushe dole ne in sami hali don Ci gaba da Gaskiya, don haka wasu mutane suna mamakin lokacin da suka sadu da ni a zahiri.
  • Ni da kaina ba na ganin wani abu mai ban sha'awa a cikin sauraron labarai kawai, sai kawai na shiga damuwa. Idan ni da kaina na shiga cikin damuwa to kun ci amanar masu saurarena ma sun karaya. Idan zan iya yin shi a hanyata kuma in sanya shi jin daɗi to zan iya yin labarai.
  • Aiki na yana buƙatar in yi kyau tsaf-tsaf, yana taimakawa don kamawa da riƙe hankalin masu kallo.
  • Yi ƙoƙarin koyon duk abin da za ku iya koya, yi amfani da duk kayan aikin da kuke da su, sannan kuma ku koyi yadda ake amfani da su. Gano abin da injiniyoyi ke yi. Gano abin da furodusoshi suke yi kuma ku koya, ku koyi sana'ar ku.
  • Ba a kwadaitar da mata a al’adar mu su rika zage-zage ko yin siyasa. Har ila yau, wasu mazan ba su shirya don zamanin mata masu mulki ba.
  • Mutane za su zarge ka ko ka yi kyau ko a’a,” Dole ne ka ji daɗin ko wane ne kai, kuma ka kasance a shirye don yin gyara da ya dace. Ranar da kuka fara sauraron sukar mutane ita ce ranar da kuka fara rayuwa ga sauran mutane. Kuma ba za ku iya yin hakan ba, har ma da rana ɗaya.