Jump to content

Wq/ha/Abdullah II na Jordan

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Abdullah II na Jordan
Musulman duniya suna taka muhimmin rawa a wajen fahimta na duka duniya. Addininmu, kamar naku, yana umurni da tausayi, zaman lafiya, da kuma haƙuri da juna.

Abdullah II bin Al-Hussein [Larabci: عبد الله الثاني بن الحسين‎, ʿAbdullāh aṯ-ṯānī ibn Al-Ḥusayn], (an haife shi 30 ga watan Junairu a shekara ta 1962), ya kasance Sarkin Jordan tun da aka naɗa shi a ranar 7 Febrerun shekarar 1999 bayan rasuwar mahaifin sa Hussein na Jordan.

Zantuka

[edit | edit source]

Jawabi ga Majalisar Turai (2015)

[edit | edit source]
Jawabi ga Majalisar Turai a Strasbourg (10 March 2015)
  • Mutane suna cigaba ne idan akwai mutunta juna. Ana gina wayewar kai ne a kan hakan. Gaba tafi kyau da ita. Amma dole a ƙulla qawance, a kara qulla ta, a kowanne zamani. Za’a iya kare abubuwa masu kyau ne kawai ta hanyar lura da kuma aiwatarwa. Wannan yana nufin fiye da matakan tsaro. Dole ‘yan-Adam su shirya kan su da dabaru, da adalci da kuma hadin kai na tattalin arziƙi da zamantakewa. A yau, waɗannan ƙalubale suna da muhimmanci na musamman. Duniyar mu tana fuskantar hare-hare na rashin imani daga ‘yan ta’adda masu dogon buri. Ƙudirin ba wai imani bane, neman ƙarfin iko ne; ƙarfin iko da ake nema ta hanyar tarwatsa ƙasashe da al’ummomi da rikice-rikicen ɓangaranci, da kuma cusa wahalhalu a fadin duniya.